**
Kai dan gadangadan ka zauna lafiya,
Kada kayi fada da kowa, kayi aiki
Aiki ba ya bata mutum sai rago,
**
Kai dan gadangadan ka zauna lafiya,
Kada kayi fada da kowa, kayi aiki
Aiki ba ya bata mutum sai rago,
Ka tashi da sa fe kada ka yi lazi,
Duniya ba ta jiran mai bacci,
Wayar ka ta yi ringing kar ka ce "sai anjima",
Arziki na wajen masu gaggawa!
**
Kai dan gadangadan ka zauna lafiya,
Kada kayi fada da kowa, kayi aiki
Aiki ba ya bata mutum sai rago,
Ka kiyaye bakin ka kada ka yi surutu,
Sirrin ka idan ya fita ya zama labari,
Kamar data na waya - idan ka yi sharing,
Gobe kowa ya san me kake boyewa!
**
Kai dan gadangadan ka zauna lafiya,
Kada kayi fada da kowa, kayi aiki
Aiki ba ya bata mutum sai rago,
Ka mutunta kowa babba da yaro,
Girmamawa ba ta kashe mutum,
Yau ka wulakanta mai shayi,
Gobe shi ne zai zama Alhaji!
**
Kai dan gadangadan ka zauna lafiya,
Kada kayi fada da kowa, kayi aiki
Aiki ba ya bata mutum sai rago,
Ka koyi sana'a kada ka dogara da waya,
TikTok da Facebook suna batar da lokaci,
Idan data ta kare kuma waya ta mutu,
Me za ka ci? Like ne?
**
Kai dan gadangadan ka zauna lafiya,
Kada kayi fada da kowa, kayi aiki
Aiki ba ya bata mutum sai rago,
Ka rike Allah a komai da kake yi,
Addu'a da gaskiya su ne gatan ka,
Idan ka bi wadannan dokoki guda biyar,
Rayuwa za ta yi maka dadi kamar fura da nono!
John G.o arose
**
Kai dan gadangadan ka zauna lafiya,
Kada kayi fada da kowa, kayi aiki
Aiki ba ya bata mutum sai rago,
**
Kai dan gadangadan ka zauna lafiya,
Kada kayi fada da kowa, kayi aiki
Aiki ba ya bata mutum sai rago,