Mata adon gari (mata),tilas muje daku komai in zakayo wallahi adole sidasu.
Rimi adon gari wannan taken garekune,
Kowa ya yadaku AJ ni zana barshine,
Duk takama isa daraja dagaku ta dangane,
Wai yaya zakace inhar kaje kaba mata.
Kowa yace daku kule mata zana amsa chas,
Ku hanashi chin kashi koda da hakoransa grass,
Inya nufokuma Dan allah kukeyimassa ass,
Dan dole zayaje yai nazar ya gane sai daku mata.
Yan kasuwa hada da sarauta dukka sai dasu,
Duk girman ma'aikata ai dole ake hada dasu,
Hatta a bangare na siyasa naga har dasu,
Jin kai da tausayi tin asali anjiyoshi gun mata.
Kune kuke damu kuma muma mu muke daku,
Juna mu tallafa atsakani namu har daku,
Koda na nesama burinsa yazoshi daf daku,
Shene na doka waka mai taken a gaidaku mata.
Fanni na rayuwata mata sun kula dani,
Nasan mahaifiya itace farkon kula dani,
Ban fasa addu'ar da nakeyimatta tin tini,
Allah yakaita jannatu firdausi maifiyata.
Bazana dakata ba adan mata nake yaba,
Sai na yabeki akan haka banijin kwaba,
Yar uwa rabin jiki yayata banni bartaba,
Duk inda zanije antina ta dayanta gun mata.
Mata chikinkune nassamu chikar farin chiki,
Tazam sinadari mahadin raina daki-daki,
In gata daf dani AJ bana bakin chiki,
Ibn sahal na kula matatache kabani duk gata.
Lissafi na arziki nan duniya to ka haifa ya,
Ni nayi shukkuran gun jalla dashi yabani ya,
Kari bugu dadi nai mata sunan mahaifiya,
Allah ya albarkacheki ki girma mu kaiki makkaranta.