Komai na nakane, Ya Yesu
Kai ne gagara misali, Ubangiji
Idan na duba baya, na ga hannunka
Kullum kana tare da ni, cikin kowane hali
Ba na jin tsoro, domin kana tare da ni
Kai ne haske na, cikin duhun dare
Zuciyata cike take da godiya
Domin ka taba rayuwata, ka canza mini
Komai na nakane, Ya Yesu
Kai ne gagara misali, a rayuwata
Babu wanda ya kai ka, babu wanda zai iya
Kai ne sarkin sarakuna, mai iko duka
Komai na nakane, Ya Yesu
Kai ne gagara misali, a rayuwata
Lokacin da nake cikin wahala
Kai ne kake karfafa ni, ka ba ni bege
Ba zan manta da alherinka ba
Kullum kana kusa da ni, mai ba ni nasara
Suna na rubuce a cikin tafin hannunka
Kai ne kariya ta, a kowane lokaci
Komai na nakane, Ya Yesu
Kai ne gagara misali, a rayuwata
Babu wanda ya kai ka, babu wanda zai iya
Kai ne sarkin sarakuna, mai iko duka
Komai na nakane, Ya Yesu
Kai ne gagara misali, a rayuwata
Ya Yesu, kai ne gagara misali (Amen)
Ya Yesu, kai ne gagara misali (Praise Him)
Zan tafi gaba, domin kana tare da ni
Babu abin da zai hana ni, in yabe ka
Glory, glory, Yesu kai ne sarki
Rayuwata a hannunka take, Ya Ubangiji
Ka shiryar da ni, zuwa ga hanyar gaskiya
Ba ni da wani buri, sai in rayu don ka
Kai ne tushen rai, kai ne kowa na
Nagode da kowace rana, da kake bani
Komai na nakane, Ya Yesu
Kai ne gagara misali, a rayuwata
Babu wanda ya kai ka, babu wanda zai iya
Kai ne sarkin sarakuna, mai iko duka
Komai na nakane, Ya Yesu
Kai ne gagara misali, a rayuwata
Komai na nakane, Ya Yesu
Kai ne gagara misali
Thank You Jesus, nagode
Amen, Amen, Amen